Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Ma'aikatar Tsaro ta Rasha, a yau Alhamis, ta bayyana cewa sojojinta sun kai hari kan cibiyar bayanai ta "Hosting UA" a Odessa, wadda ta kasance ana amfani da ita wajin sarrafa bayanan leƙen asiri da sabis na sojojin Ukraine.
Ma'aikatar a cikin wata sanarwa ta ce: "An kai hari kan cibiyar "Renta Logistics" ta sufuri da kayan aiki a Kiev, inda aka kafa wani ɗakin aiki don kera kwale-kwalen marasa matuƙa."
Haka kuma sojojin Rasha sun kai hari kan wani jirgin ruwa, wanda ke ɗauke da kayan soji da kayayyaki masu amfani biyu ga sojojin Ukraine a tashar jiragen ruwa ta Chornomorsk.
Rasha Ta Harbo Jiragen Mara Matuƙa 330 Na Ukraine
Haka kuma, Na’urorin tsaron sama na Rasha sun lalata jiragen marasa matuƙa 330 na Ukraine cikin dare a lardunan Bryansk, Belgorod, Smolensk, Kaluga, Tula, Kursk, Tver, Lipetsk, Oryol, Tambov da Astrakhan, da lardin Moscow da jamhuriyar Crimea da kuma a kan Tekun Baƙi.
Jiya Laraba ma, Na’urorin tsaron sama sun harbo bama-bamai uku na sama masu jagora, da makami mai linzami na tsarin "HIMARS" na Amurka, da jiragen mara matuƙa 768 masu tsayayyen fikafi.
……………..
Ra'ayinka